fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Rivers, Rochas Okorocha

Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha, kuma ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

EFCC ta tafi da Rochas daga gidansa da ke unguwar Maitama a Abuja da yammacin Talata.

Jami’an EFCC da ƴan sanda sun yi dirar mikiya tare da mamaye gidan tsohon gwamnan, inda rahotanni suka ce an yi harbi a ƙoƙarin kama shi.

Hukumar EFCC ta ce matakin ya biyo bayan ƙin amsa gayyatar da tsohon gwamnan ya yi bayan tsallake belin da ya samu a farko.

A ranar 24 ga watan Junairun shekarar 2022 ne EFCC ta shigar da kara a gaban kotu tana tuhumar Okorocha da laifuka 17 da suka hada da karkatar da kudaden al’umma da kadarori da suka kai naira biliyan 2.9.

Karanta wannan  Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya shilla kasar Turkiyya don shakatawa

Hukumar ta ce yunƙurin gurfanar da Sanata Okorocha sau biyu ya ci tura sakamakon ƙin amsa gayyatar da aka yi ma shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.