Hukumar EFCC ta kama mutane 30 da ake kyautata zaton ‘yan damfara ne a jihar Abuja ranar talata.
Kuma mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya bayyana cewa sun kama su ne a yankin Lugbe da Kubwa.
Inda yace sun kwace motoci a hannunsu wanda suka hada da Mercedes Benz, lexus, Toyota da dai sauran su tare da wayoyi da kofutoci.
Kuma yace suna cigaba da bincike akan kansu kafin a gurfanar dasu a gaban kulliya.