Shugaban hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC, Abdulrashid Bawa ya bayyana cewa, zasu fara binciken inda ‘yan takara ke samo kudin sayen fom din miliyan 100 na takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a Channels TV.
Yace bibiyar irin wannan lamari hakkin hukumar zabe me zaman kanta, INEC ne, yace amma zasu yi aiki tare da INEC dan magance matsalar.
Zuwa yanzu, jam’iyyar APC ta tare Naira Biliyan 21.93 daga ‘yan takarar shugaban kasa, 22 da kuma ‘yan takarar gwamna 105 da suka sayi fom don takara.
Hakanan akwai ‘yan takarar majalisar tarayya, 1198 da suma suka sayi fom din.