fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

EFCC tace zata fara yankewa masu ba ‘yan Yahoo Boys hayar gidaje hukuncin shekaru 15 a gidan yari

Hukumar dake yaki akan sata da damfara ta EFCC ta bayyana wata hanya guda da zata fara kawo karshen ‘yan damfarar yanar gizo a kasar, watau Yahoo Boys.

Inda hukumar tace zata fara yankewa masu gidajen haya shekaru 15 a gidan yari idan har suka cigaba da ba ‘yan Yahoo Boys hayar gidaje.

Ta bayyana hakan ne gami da babban taron da zata gudanar yau laraba da misalin karfe shida na yamma, inda tayiwa taron lakabi da ‘Zamu yankewa masu ba ‘Yahoo Boys haya hukuncin shekafu 15 a gidan maza.’

Leave a Reply

Your email address will not be published.