fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Erling Haaland ya amince ya koma Manchester City, inda zai zamo dan wasan dayafi daukar albashi mai tsoka a tarihin gasar Firimiya

Tauraron dan wasan Borussia Dortmund, Erling Braut Haaland na shirin barin kungiyar tasa a karshen wannan kakar, yayin da manyan kungiyoyin nahiyar turai ke harin sayen shi.

Wanda suka hada da Manchester City, Real Madrid, Barcelona da kuma Paris Saint Germain.

Manema labarai na Daily Mail sun ruwaito cewa dan wasan ya amince ya koma City, yayin da kungiyar ke shirin mayar da shi dan wasan dayafi kowa daukar albashi mai tsoka a tarihin gasar Firimiya.

Inda take shirin biyan shi sama da yuro 500,000 a kowane mako kuma hakan zai aa ya kerewa cristiano Ronaldo.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.