fbpx
Friday, October 23
Shadow

Everton 5-2 West Brom: Yayin da James Rodriguez yaci kwallon ta farko a Eveton shi kuma Calvert yaci Hat Trick

A yau kungiyar Everton ta karbi bakuncin West Brum yayin da suka lallasa bakin nasu bayan Calvert Lewin yayi nasarar cin Hat Triick karo na farko wanda hakan ya taimakawa kungiyar tashi tayi nasarar cin 5-2 tsakanin su da yan wasa goma bayan an ba Kieran Gibbs jan kati kuma har alkalin wasan ya korin kocin West Brom Slaven Bilic.

Calvert Lewin ya taka muhimmiyar rawa sosai a wasan yayin da shima tsohon dan wasan Real Madrid James Rodrigues ya ci kwallon shi ta farko a Everton kuma ya kasance a cikin rikicin daya sa aka baiwa Kieran Gibbs jan kati. Everton yanzu tayi nasara a gabaya wasannin ta uku data buga yayin ita sabuwar kungiyar Premier League West Brom take neman maki na farko a gasar.
West Brom ne suka fara jagorantar wasan bayan Grady Diangana ya ci masu kwallo guda kafin Calvert ya zira kwallon shi ta farko kuma James ya kara wata kwallon amma Piereira ya ramawa kungyar West Brom kwallon. Amma daga baya Michael Kaene yaci kwallo guda shi kuma Calvert ya kara zira kwallaye biyu wanda Everton tayi nasara a wasan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *