fbpx
Monday, August 8
Shadow

Fadar Gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudinta daga Biliyan 15 zuwa Biliya 10

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa ta rahe kasafin kudinta na shekarar 2021 zuwa Biliyan 10 daga Biliyan 15 a shekarar 2020.

 

Hakan ya fito ne daga Ettah Esah, daraktan yada labarai na fadar shugaban kasar. Esah ya bayyana cewa  Babban daraktan fadar shugaban kasar, Dr. Tijjani Umar ne ya jagoranci zaman tattaunawa tsakanin ma’aikatun gwamnati ranar Asabar din data gabata inda aka yanke wannan hukunci.

Hakan na zuwane bayan umarnin da ministar kudi da tsara kasafin kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayar na ma’aikatun gwamati su hada kasafin kudinsu na 2021 dan aikawa ga majalisar Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.