fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Fadar shugaba Buhari zata kashe Miliyan dari hudu kan kula da janareta, da kayan daki da sauransu

Fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari zata kashe Naira Miliyan 402.2 wajan kula da janareta da kayan katako na daki da sauransu.

 

Hakan na kunshene a cikin kasafin kudin shekarar 2022 wanda ya nuna kudin zasu hada da kula da fadar dadai sauran abubuwan Amfani.

 

Hakanan kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mataimakinsa,  Farfesa Yemi Osinbajo zasu kashe Naira Biliyan 3.087 wajan tafiye-tafiye a ciki da wajen Najeriya.

 

Hakanan shugaban zai kuma kashe Miliyan 301 wajan cin abinci, akwai kuma alawus na taruka da ya kai Naira Miliyan 174.176 da shugaban kasar zai samu.

Karanta wannan  Majalissar dinkin duniya tace harkar Crypto zata iya rusa Najeriya da sauran kasashen da suka cigaba

 

Hakanan kuma shugaban zai kashe Naira Miliyan 503 wajan sayen katin wata, da shiga yanar gizo da biyan kudin wuta dana ruwa, da gyaran kwata.

 

Shugaban zai kuma kashe Miliyan 470 wajan sayen magani, Jarida, Litattafai, da biro da takarda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.