fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Faduwar farashin man fetur ya hanani cimma burina>>Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya zargi kungiyar tsageran Naija Delta da kuma faduwar farashin man fetur a matsayin abubuwan da suka kawo mai cikas wajan cimma burinsa.

 

Shugaban ya bayyana hakane a Borno, yayin ziyarar aiki da ya kai inda ya kaddamar da wasu ayyukan da gwamnan yayi.

 

Shugaba Buhari yace kamin ya hau mulki ana sayar da man fetur akan Dala $100 kowace Lita kuma ana samun ganga miliyan 2.1 a kullun.

 

Yace amma bayan hawansa mulki, Man fetur din ya dawo kan Dala $36 akan kowace Lita da kuma tsageran Naija Delta suka rika fasa bututun man.

Karanta wannan  Gurbatattun shuwagabanni ne ke yawo da dakarun tsaro bayan sun sauka a mulki, cewar gwamna Wike

 

Yace hakan zai nuna maka cewa, lallai wannan gwamnati ta yi kokari sosai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.