Rahotanni sun bayyana cewa farashin gangar danyen mai na Duniya da ake kira da Brent ya kara faduwa kasa inda ya koma Dala 19.
Akan farashin Brent ne ake sayar da dayen man Najeriya.
Farashin danyen man na ci gana da faduwa kasa duk da rage yawan danyan man da kasashe kungiyar OPEC sukayi. Hakan baya rasa nasaba da rashin bukatar sayen man daga kasashen da yawanci suke kulle saboda dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.
Najeriya dai ta rage farashin danyen man data yi kasafin kudinta akai daga Dala 57 zuwa dala 30.
Kasar Saudiyya ta bayyana cewa tana kallon yanda farashin man ke gudana kuma zata dauki mataki.