fbpx
Friday, July 1
Shadow

Farashin Danyen Mai ya fadi a kasuwar Duniya

Farashin Danyen Mai fadi a kasuwannin Duniya a jiya, Juma’a inda yayi kasa da kaso 2 cikin 100. Hakan baya rasa nasaba da karuwar cutar Coronavirus/COVID-19 a fadin Duniya.

 

Brent ya fadi da kaso 2.9 inda aka sayar dashi akan Dala 41.92, wanda kuma akan wannan farashine ake sayar da danyen Man Najeriya.

Kasar Amurka dai da itace tafi kowace kasa sayen Man a Duniya na ci gaba da fuskantar matsalar Annobar cutar Coronavirus/COVID-19.  Hakanan wasu sauran kasashen masu karfin tattalin arziki suma cutar na yawaita inda ake kara saka dokokin hana zirga-zirga.

 

Wasu masana sun ce babu tabbacin yanda kasuwar man zata kasance nan gaba, kamar yanda Reuters ta bayyana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.