Sunday, May 31
Shadow

Farashin Danyen mai ya kara faduwa a kasuwar Duniya

Farashin gangar danyen mai na Brent, wanda akanshine ake sayen man Najeriya, ya samu faduwa da kaso 0.9 inda ya koma ana sayar dashi akan Dala 30.68 sannan shima na kasar Amurka ya samu faduwar kaso 0.7 inda ya koma ana sayar dashi akan 24.57.

 

Farashin danyen man ya dan farfado a makonni 2 da suka gabata,kamar yanda Reuters ta ruwaito kuma hakan baya rasa nasaba da bude wasu kasashe da aka yi na wucin gadi.

 

Kasashen da basu bude ma ba suna bayyana cewa zasu bude bayan kulle kasashen da aka yi dan dakile cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Saidai masana sun ce kasuwar mai zata ci gaba da ganin matsala har zuwa shekarar 2021 saboda akwai wata sabuwar cutar Coronavirus/COVID-19 dake nuna alamun bayyana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *