fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Farashin danyen mai ya tashi zuwa Dala 40 a kasuwannin Duniya

Rahotanni sun bayyana cewa, Farashin Danyen Mai ya tashi zuwa Dala 40 a kasuwannin Duniya.

 

Farashin ya samu tagomashin kaso 2 cikin 100 ne wanda aka sayar da Brent akan Dala 40.53, kamar yanda Reuters ta tabbatar.

Ana tsammanin rashin kyawun yanayi na kasar Amurka da ya hana kasar ayyukan hakar manta yanda ya kamata ne yasa farashin ya tashi sama.

 

Saidai masana sun bayyana cewa bukatar man zata ci gaba da raguwa saboda har yanzu kasashe basu kammala farfadowa daga matsin tattalin arzikin da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta zo dashi ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *