fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Farashin gangar mai ta kara faduwa zuwa dala 15

Rahotanni sun bayyana cewa, farashin gangar danyen mai na Brent wanda da shine akewa man Najeriya farashi ya kara faduwa zuwa Dala 15.98 kamar yanda Reuters ta ruwaito.

 

Wannan shine farashi mafi karanci da man ya taba kaiwa tun shekarar 1999, kusan shekaru 21 kenan.

 

Rahoton yace man ya dan farfado inda aka rika sayar dashi akan Dala 16.63.

 

Rahoton ya kara da cewa farashin man ya fadi da kashi 80 cikin 100 a shekararnan saboda Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 data mamaye Duniya kuma ta yi sanadin mutuwar mutane kusan 180,000.

 

Yawan man da ake kaiwa kasuwar Duniyar ya zarce bukatar man da ake dashi, sannan kasar da ta fi kowace yawan samar da kaya,Amurka na faman neman inda zata ajiye rarar man da take dashi.

 

Man Amurka dai yayi faduwar da ba’a taba gani ba a Duniya wanda sai da aka sayar dashi a kasa da Dala 0.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *