fbpx
Friday, July 1
Shadow

Farashin gas ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 cikin wata biyar a Najeriya

Farashin gas din girki ya karu da kashi 25 cikin 100 tsakanin Janairu zuwa watan Mayun 2022 a sassa da dama na Najeriya.

Wani bincike ya nuna cewa kilo 12 na tukunyar gas da ake sayarwa kan naira 7,500 a watan Janairu ya karu zuwa naira 10,500 a birnin Lagos da Abuja da sauran manyan birane.

Wannan yanayi da ake ciki ya tilastawa magidanta neman zabin girki ko koma hura itace da sayen kalanzir.

Shugaban kungiyar dilalan man fetur da iskar gas na kasa, Mista Michael Umudu, ya ce akwai matukar damuwa kan abin da ke faruwa tsakanin masu sari da kuma daidaikun da ke saye domin amfanin gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published.