fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Farashin kayan abinci ya karu da kashi 42 cikin wata 12 a Najeriya>>NBS

Wani sabon rahoto da hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa farashin wasu kayan abinci ya karu da kashi 42 cikin dari a shekara daya a kasar.

Rahoton, wanda aka yi wa lakabi da “Sanya ido kan wasu kayan abinci zuwa watan Afrilun 2022” ya bayyana cewa farashin kilogiram daya na wake (fari da baci) ya tashi da kashi 44.32, wato daga N359.64 a watan Afrilun 2021 zuwa N519.05 a watan Afrilun 2022.

Kazalika farashin kilogiram daya na doya ya tashi da kashi 42.88, daga N252.80 a watan Afrilun 2021 zuwa N361.20 a watan Afrilun 2022.

Karanta wannan  Darekta janar na kungiyar dake yiwa Tinubu yakin zabe ya mika sakon dogiya ga gwamnonin Arewa saboda goyon bayan shugaban kasa na gaba na sukeyi, a cewarsa

Haka kuma farashin kwalba daya na manja ya tashi da kashi 45.59, daga N578.86 a watan Afrilun 2021 zuwa N842.75 a watan Afrilun 2022.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.