Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, farashin kayan abinci yayi tsada da yawa a fadin kasarnan inda ta bayyana shirin daukar mataki dan kawo saukin matsalar.
Ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka inda tace zasu yi zaman taron gaggawa dan ganin an kawar da matsalar tsadar abinci.
Ta kuka kara da cewa, Najeriya ta samu habakar tattalin arziki da kaso 3.1 cikin 100 idan aka kwatanta da wanda ta samu a shekarar data gabata na kaso 0.5 cikin 100.
Ta kuma bayyana amincewa da bayar da Biliyan $3.1 ga hukumar Kwastam dan sabunta ayyukanta zuwa na zamani.