fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Fashewar tankar dakon mai ya lakume rayukan mutane 12 a Osun

Akalla mutane 12 ne rahotanni suka bayyana cewa sun kone kurmus sanadiyyar fashewar tankar dakon mai wanda ya faru a kan babbar hanyar Ilesa-Akure, A jihar Osun, ranar Litinin.

Hatsarin wanda ya afku a Erin-Ijesha, wani gari da ke karamar hukumar Oriade ta jihar, ya jefa mazauna yankin cikin wani yanayi na jimami.

Rahotanni sun bayyana cewa, motar dakon mai din, bayan ta fadi ta kwaranyar da abin da ke cikinta a kasa, wanda hakan ya haifar da conkoson ababan hawa a kan babbar hanyar.

 

Jaridar Tribune ta rawaito cewa fashewar tankar wanda ya faru da rana ya kara cunkoson ababen hawa kafin isowar jami’an kashe gobara da jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) wadanda daga karshe suka shawo kan al’amura.

Karanta wannan  Tekun Legas ya tafi da dalibai hudu da suka je murna bayan sun lashe jarabawar WAEC

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa ya dauki ma’aikatan kwana-kwana  awanni kafin su kashe wutar. Hakanan suma jami’an hukumar kiyaye haddura sun dauki lokaci mai tsawo kafin su shawo kan halin da ake ciki.

A cewarsa, sa Mutane da dama sun rasa ransu yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yemisi Opalola, ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce hukumar bata gama tantance yawan wadanda lamarin ya shafa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.