fbpx
Friday, August 12
Shadow

Fasto Bakare soki Kiristocin dake kalubalantar tikitin APC, yace tsayar da Musulmai da jam’iyyar tayi ba laifi bane

Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa yana goyon bayan tikitin APC duk da musulmi ta zaba a matsayin ‘yan takararta da kuma mataimakinsa na shugaban kasa.

A watan Mayu Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar wanda shima Tunde ya tsaya takarar amma ko kuri’a daya bau samu ba.

Wanda a wannan watan Bola Ahmad Tinubu ya bayyana tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Hakan ya jawo cece kuce tsakanin Kiristicin Najeriya sosai, amma yanzu fasto Tunde yace masu kar su damu babu matsala domin ba ayi hakan don a muzguna masu ba salon siyasa ne kawai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.