fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Fasto Giwa yace shaidan ne ya ziga Tinubu ya zabi Musulmi a matsayin abokin takararsa

Babban faston Najeriya, Adewale Giwa ya bayyana cewa shaidan ne ya ziga dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya zabi Musulmi, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Inda yace APC ta tafka babban kuskure kuma dole ta girbi abinda ta shuka saboda Kiristoci ba zasu taba zabar taba domin basu da adalci.

Ya kara da cewa wannan lokacin ne ya kamata ‘yan Najeriya su san ‘yancin su kuma idan har basu kwace shi yanzu ba to ba zasu taba samun ‘yancin ba har abada.

Karanta wannan  APC ta gaza domin shugaba Buhari bai damu da ilimin Najeriya ba, cewar daliban Najeriya

A karshe yace yaji wasu ‘yan APC na cewa ai cece kucen da Kiristoci keyi na wani dan lokaci ne, wannan maganar labarai ne suna nan akan bakar su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.