fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Fasto ya yiwa mace me ciki fyade bayan da ta je ya mata addu’a

Hukumar ‘yansanda ta jihar Ondo sun kama wani fasto da yawa mace me ciki fyade.

 

Matar ta je wajan fastonnne ya mata addu’a amma shine ya bude da mata fyade.

 

Matar me suna Bukola tace faston ya fara goga mata wani man da yace na tsarkakewa ne a gabanta, sannan ya fara lalata da ita.

 

Tace ya mata karyar wai dan dake cikinta ba daidai yake kwance ba, inda yace man da yake goga mata ana bukatar ya shiga ta cikin al’aurarta.

Karanta wannan  Majalissar dinkin duniya tace harkar Crypto zata iya rusa Najeriya da sauran kasashen da suka cigaba

 

Tace dan hakane yace zai yi amfani da al’aurarsa ya tura mata tunda mijinta bayanan, tace sai bayan da ya gama sannan hankalinta ya dawo jikinta.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Mrs Funmilayo Odunlami ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa suna kan binciken me laifin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.