Wani fasto dan jihar Kaduna, David Azzaman ya sha alwashin samarwa Peter Obi kuru’u miliyan guda a jihar.
Faston ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai, inda yace ba zasu zabi jam’iyyar data zabi ‘yan addini guda ba.
Ya kara da cewa abokin takarar Tinubu Baba Ahmad Musulmi ne dan Zaria saboda haka su zasu zaba.
Kuma zai samarwa dan takarar shugaban kasar na Labour Party kuru’u miluyan guda a jihar Kaduna.