fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Femi Fani Kayode ya bukaci Daily Trust ta biyashi Biliyan 6 saboda zargin bata suna

Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode ya bukaci jaridar Daily Trust data biyashi diyyar Biliyan 6 saboda zargin bata suna.

 

Daily a wata caccaka da wani Iliyasu Gadu ya rubuta kuma ta wallafa wanda lamarin ya dauki hankula sosai ta bayyana FFK a matsayin dan kwaya wanda har kasar Ghana ya je neman magani amma har yanzu be warke ba.

Da yake magana akan wannan rubutu ta bakin  Lauyansa, Adeola Adesipe, FFK ya bayyana cewa wannan abu ya sa sunansa ya baci dan haka ya baiwa Daily Trust kwanaki 14 ta cire labarin sannan ta bashi hakuri ta kuma buga a sauran wasu gidajen Jaridu 2 da kuma biyanshi Biliyan 6 in ba haka ba zai garzaya kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.