fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Femi Kayode da Shehu Sani sunyi tsokaci kan kashe mutane 43 da garkuwa da ‘yan kasar sin da ‘yan bindiga suka yi a jihar Niger

Taohon ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani Kayode yayi Allah wadai da kashe mutane 43 da ‘yan bindiga sukayi tare da garkuwa da wasu ‘yan kasar sin guda hudu dake hako gwal a jihar Niger.

Ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter inda yace Allah yajj qan mutanen da suka rasu kuma mika sakon ta’aziyya ga gwamna  Bello na jihar.

Ya kara da cewa ya kamata a kamo ‘yan bindigar da sukayi wannan ta’addancin kuma a hukunta su.

Inda shima tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani yayi tsokaci akan lamarin yace abin yayi muni sosai domin hadda sojoji aka kashe da ‘yan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published.