Mataimakin shugaban budaddiyar jami’ar Najeriya wanda aka fi sani da National Open University of Nigeria (NOUN), Farfesa Abdallah Uba Adamu ya rasa mahaifinsa, Dr Uba Adamu a ranar Litinin.
Dr Uba Adamu ya mutu bayan gajeriyar rashin lafiya a wani asibiti a Kano yana da shekara 85.
Za a gudanar da sallar jana’izar a gidan mamacin a Kawo, Nassarawa GRA, ranar Talata da karfe 8 na safe.
Mirgayin yayi karatun digirinsa na farko a jami’ar Ahmadu Bello dake zariya, sannan yayi daktarin digirin sa a Jami’ar Bayero dake kano, inda yayi koyarwa a makaranta polytechnic kafin yayi ritaya.