fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Rahama Sadau ta caccaki wani mutum da ya soki fim din hausa na farko da ta shirya(Rariya)

Da alama fitacciyar korarriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau bataji dadin sukar da wani bawan Allah ya yiwa fim din Hausa na farko data shirya da kantaba me suna Rariya, an ga wasu sakonnin mayar da martani da Rahamar ta wallafa a dandalinta na sada zumunta da muhawara na Twitter, inda take cewa “kana tunanin zan damu dan ka soki fim dina?, kai kadaine fa….a’a(bazan damuba).

A cikin wani rubutun da tayi Rahamar tace “Idan beyi maka ba yayi ma wasu…kunyi rubutu nayi banza, amma dai dole akeso sai nayi magana shine aka kara yin wani”.

Bayan da aka koreta daga masana’antar fina-finan Hausane Rahamar ta koma gefe ta shirya fim din Rariya wanda ya samu wakar da ta sayar dashi tun kamin ya fito, wadda sanannen mawakin Hausar nan Nura M. Inuwa ya rera.

Fim din Rarariya yayi zarra a tsakanin fina-finan Hausa na wannan shekarar da aka fitar inda ya lashe kyautar fim din Hausa na shekara da yafi yin fice a wannan shekarar.

Karanta wannan  Kalli Bidiyo: Shi Ma Fa Aminu Ya Ci Kudin Talakawa Domin An Dana Shi A Jirgin Gwamnati

Saidai kuma ba lallaine duk kyan abuba ace kowa da kowa yayi na’am dashi ba, haka kuma ba lallaine duk munin abuba ake kowane be sonshiba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *