Firaministan Israela Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, harin da suka kai kan sansanin ‘yan gudun Hijira wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 50 kuskurene.
Ya bayyana hakane amma kuma yace zasu ci gaba da yaki dan tabbatar da sun samu nasara akan ‘yan ta’dda.
Ya bayyana cewa amma kuma sun san cewa kuskurene harin da suka kai kuma suna bincike akan lamarin.
Harin dai ya fuskanci Allah wadai daga bangarori daban-daban na Duniya.
[…] Lamarin ya jawowa kasar Israela Allah wadai wanda daga baya Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya fito yace kuskurene kuma suna bincike akai. […]