Fusatattun matasa sun babbaka wasu mutane biyu a jihar Enugu ranar litinin bayan da aka zarge su da yiwa yarinyar ‘yar shekara goma fyade.
Kuma sun kashe yarinyar sun jefar da ita a daji yayin da suka cire mata wasu sassan jikinta.
Wannan lamarin ya faru ne a karamar hukumar Nsukka dake jihar ta Anambra kuma wani mazaunin yankin ne ya bayyanawa manema labarai wannan labarin.