fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Fusatattun matasa sun babbaka mutumin daya yi garkuwa da malamin majami’ar Katolika ta jihar Edo

Fusatattun matasa sun babbaka daya daga cikin mutanen da sukayi garkuwa da malamin majami’ar Katolika ta jihar Edo, Rev Fr Christopher Odia.

Matasan sun bi masu garkuwa da mutanen ne bayan sunyi garkuwa da shi ranar lahadi, inda har suka bude masu wuta suka kashe mutun guda suka jiwa wasu uku rauni.

Amma duk da hakan sai da matasan sukayi nasarar damke biyu daga cikin ‘yan ‘taddan inda suka babbaka guda kafin hukumar ‘yan sndan ya ceci dayan a hannun su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.