Fusatattun matasa sun babbaka wani matashi wanda ya kasance barawon janareta a jihar Abia.
Matashin ba a san sunan saba kuma basu san daga ina yake ba, amma duk da haka sun babbaka shi kan satar janaretan daya yi masu.
Manema labarai na ABN ne suka ruwaito wannan labarin.
Inda rahoton ya kara da cewa matashin tare da abokansa guda biyu ne suka je yankin suna kokarin satar janareta yayin da ake damkesa aka babbaka shi.
Kuma sun kasance suna addabar al’ummar yankin da satar janareta a lokuta da dama.