Wasu fusatattun matasa sun babbaka wani mutumin da ake zargi dan garkuwa da mutane ne a Obasi dake karamar hukumar Idimili a jihar Anambra.
An samu labari cewa yana daya daga cikin ‘yan ta’adda hudu dake ta’addanci a anguwar.
Kuma wannan lamarin ya faru ne ranar alhamis da daddare inda matasan anguwar ka yawo tare hukuma yayin da suka ga motar tasa suka bukaci ya budeta su duba.
Kwatsam sai sukaga mata da miji da akayi garkuwa dasu kwanan nan a cikin motar, wanda hakan yasa suka fara aman wuta a tsakanin su har sukayi nasara akan sa suka babbaka shi.
Kuma gawar tashi tana nan akan hanya har ranar juma’a da yamma ba wanda ya dauke ta.