fbpx
Monday, August 15
Shadow

Fusatattun matasa sun tare babbar hanyar Abia sunyi zanga zanga kan kashe wani makiyayi da shanayensa a jihar

Wasu fusatattun matasan Arewacin Najeriya sun tare babbar hanyar jihar Abia sunyi zanga zanga bayan kashe wani makiyaye da shanayensa da ‘yan bindiga suka yi.

‘Yan bindigar sun kashe shine a kasuwar shanaye ta Lokpata dake jihar ta Abia, wanda hakan yasa daruruwan matasan Arewa suka yi zanga zanga kan wannan kisan.

Matasan sun bayyana cewa bazasu laminci wannan abin ba dole gwamnati tayi wani akai domin wannan cin zarafi na.

Wasu mazaunan jihar ta Abia dama sun bukaci a mayar da kasuwar wani wurin na daban domin ‘yan bindiga suna gudanar da ta’addancinsu a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.