‘Yansanda a jihar Katsina sun kama wasu masu garkuwa da mutane yayin da suke karbar kudin fansa.
Lamarin ya farune a karamar hukumar Malunfashi inda aka kama Saifullahi Usman yayin da yake shirin karbar kudin fansar.
Yawa shafi’u Muhammad barzanar cewa, idan bai bashi dubu 50 ba, zai saceshi ko kuma wani danginsa.
Saidai shafi ‘u ya sanar da ‘yansanda inda aka hada baki kawa mai garkuwar kofar rago aka kamashi.
Hakanan ‘yansandan sun kama wani Muhammad Ibrahim shima a karamar hukumar Kafur inda ya aikewa da wani bawan Allah takardar barazana ya biyashi dubu 100 ko kuma a saceshi.
Hukumar ‘yansandan tace har yanzu suna kan bincike.