fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Fyade na Masa: Matar aure da boka ya dirkawa ciki ta bayyana

Wata matar aure da bokan da take zuwa wajansa neman sa’a ya dirkawa ciki, tace tabbas ita ta tursasashi.

 

Matar me suna Shadiat ta bayyana cewa shekararsu 8 da mijinta amma har yanzu bata haihu ba, tace shine ta je wajan Bokan tace yayi lalata da ita ko ta gane cewa rashin haihuwar daga wajanta ne ko kuwa?

 

Shima Bokan, Lamidi Ifaloba, ya bayyanawa The Nation cewa ranar matar taje dakinsa da gudu tace mijinta ne ke dukanta.

 

Yace da yake ana ruwa sai ya ce ta kwana da safe sai ta koma gida tunda dare yayi, yace suna hakanr ya je fita daga dakin kawai sai matar ta jawoshi tace yayi lalata da ita.

 

Yace yaso yin ihu amma sai ya tuna kar asirinsu ya tonu dan dama a baya an taba masa irin wannan zargin.

 

Yace hakanan ya daure yayi lalatar da ita.

 

Yace kwana biyu sai gata ta zo tace masa tana da ciki bayan lalatar da suka yi, yace ya jima bai ganta ba, sai lamuransa suka fara ja baya.

Karanta wannan  Na gaji da daukar nauyin kaina aure nake nayi, cewar tauraruwar Nollywood

 

Yace da yayi bincike sai tsafinsa ya nuna masa cewa, ai saibya karbo yaron da matar can ta haifa masa idan yana son zaman lafiya, yace shine ya je ya gayawa iyayen matar abinda ya faru.

 

Iyayen sun amsa masa cewa, lallai sun san dan nashi ne kuma zai koma hannunsa nan ba da jimawa ba.

 

Shima mijin, Sikiru Olaleye ya bayyana cewa makwabtane suka fara gaya mada cewa dan fa ba nashi bane na bokan da matarsa ke zuwa wajansa ne, yace yayi mamaki dan kuwa yasan yana gamsar da matarsa da jima’i.

 

Yace kuma yana da yara da ya haifa da tsohuwar matarsa dan haka ba zai yiyu ace bai haihuwa ba.

 

Yanzu dai matar ta yi yaji kuma yayi yayi ta dawo ta kiya, saidai bayan da ya ji cewa ta ci amanarsa, ya fita batunta.

 

Lamarin ya farune a kauyen Malaka dake karamar hukumar Owode-Obafemi a jihar Ogun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.