Ƙungiyar Ƙasashen G7 masu ƙarfin masana’atu sun amince a yi amfani da ribar kadarorin Rasha da aka ƙwace, domin bai wa Ukraine ta yi amfani da su.
Biden ya ce yarjejeniyar za ta hada da tura bayanan sirri, da bai wa sojoji horo da bin dokokin NATO da zuba kuɗi a masana’antu da ke Ukraine domin ci gaba da samar da makamai.
Biden ya ce burinsu shi ne samar wa Ukraine tsaro ”na gaske”, da kuma turmusa hancin Rasha da ƙawayenta a ƙasa.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wannan ba abu ne da Shugaba Putin zai kawar da kai ya kyale ba.