fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Ga jerin abubuwan da Hukumar JAMB ta hana dalibai su shiga dakin jarawaba da su

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a a Najeriya, JAMB ta bayyana abubuwan da ba za a bari dalibai su shiga da su dakunan rubuta jarabawa ba.

JAMB ta wallafa jerin abubuwan ne a shafinta na intanet. Ta kuma ba masu shirin rubuta jarabawar shawara, tana cewa kar su kuskura su kai wadannan kayayakin kusa da dakin rubuta jarabawar.

“Duk wanda ya yi biris da wannan shawarar, ba za a bari ya rubuta jarabawarsa ba”, inji hukumar.

Hukumar ta JAMB ce ke shirya jarabawar da ke ba dalibai damar shiga jami’o’in kasar.

Ranar 6 ga watan Mayun nan zuwa ranar 16 ga watan za a gudanar da jarabawar a fadin kasar.

Karanta wannan  YANZU-YANZU: KASU ta bukaci dalibai su gaggauta komawa makaranta kuma zata hukunta masu fashi

Ga jerin abubuwan da JAMB ta hana masu son rubuta jarabawa shiga dakunan jarabawar da su:

  • Alkaluman rubutu
  • Wayar salula ko ma dukkan na’urorin sadarwa na latironi
  • Gilasai masu kyamara da ake leken asiri da su
  • Na’urar lissafi, wato kwakuleto da ire-irensu
  • Kyamarori da naurorin nadar sauti da makurofo da earpiece na sauraron sauti
  • Dukkan wani littafi ko kasida ko abin karatu da rubutu

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.