Tuesday, December 3
Shadow

Ga masu cewa basu ga dalilin dawo da tsohon taken Najeriya ba, ku sani dawo da taken Najeriyar na daya daga cikin muhimman aikin da nake son yi>>Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, dawo da taken Najeriya na daya daga cikin muhimman abubuwan da yake son yi a mulkinsa.

Ya bayyana hakane a yayin ganawa da kungiyar dattawan Najeriya, ACF.

Tinubun dai ya sakawa dokar data dawo da tsohon taken Najeriya hannu wanda hakan ya jawo cece-kuce inda mutane ke cewa ba wannan ne matsalar kasar ba.

Shugaba Tinubu ya kuma jawo hankali kan samun hadin kai a Najeriya.

Karanta Wannan  Kungiyar 'yan kasuwar man fetur, IPMAN ta yi baranzanar tsayar da aiki saboda karin kudin man feturninda tace hakan ya kara jefa 'yan Najeriya wahala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *