fbpx
Monday, December 5
Shadow

Ga wani gari shima a kasar Switzerland da idan ka yadda ka koma da zama za’a biyaka makudan kudade

Garin Albinen na kasar Switzerland inda ake biyan mutane kudi in sum koma da zama-boredpanda
Wannan wani kauyene a kasar Switzerland da ake kira da suna Albinen, mutanen kauyen, musamman matasa, duk sun tsere, sun koma birni, mutanen dake zaune a kauyen yanzu duka-duka basu wuce su dari biyu da arba’in ba. saboda babu dalibai, har makarantar kauyen an kulleta.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Yanzu gaba daya yaran dake kauyen su kwaine kacal. Kauyen Albinen yana neman mutane da zasu koma can garin da zama din-din-din, kuma idan ka yadda ka koma akwai kyautar kudi masu tsoka da za’a baka, kasar Switzerland na daya daga cikin kasashen Duniya masu karfin tattalin arziki, da yawa masu kudi da ‘yan kasuwa suna kai ajiyar kudadensu kasar.

Garin Albinen na kasar Switzerland inda ake biyan mutane kudi in sum koma da zama-boredpanda
Mutum me cikken hankali, idan ya koma kauyen Albinen za’a bashi kyautar kudi dalar Amurka dubu ashirin da biyar wanda a kudin Najeriya sun kai kwatankwacin naira miliyan tara, yaro wanda be balaga kuma za’a bashi dalar amurka dubu goma wanda a kudin Najeriya sunkai kwatankwacin naira miliyan uku.
Garin Albinen na kasar Switzerland inda ake biyan mutane kudi in sum koma da zama-boredpanda

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sharadin komawa wannan gari da kuma samun waccan garabasa sune, kada shekarunka su wuce 45, sannan kuma sai in ka yarda zaka zauna a garin din-din-din, sannan kuma dole sai ka zuba jari a garin daya kai dalar Amurka dubu dari biyu wanda a kudin Najeriya sun kai kwatankwacin naira miliyan saba’in da biyu(watau tun daga kudin da zaka kashe wajan saye ko gina gida, da kuma,watakila, kasuwancin da zaka rika yi dan samun kudi).
Garin Albinen na kasar Switzerland inda ake biyan mutane kudi in sum koma da zama-boredpanda
Amma duk da haka akwai riba fa, ka dauka cewa misali kana da mata hudu da ‘ya’ya da suka kai goma, kagana za’a baka kudi dalar amurka dubu dari biyu da ashirin da biyar kenan wanda a kudin Najeriya sun kai kwatankwacin naira miliyan tamanin da daya, kaga ka mayar da kudinka, hadda riba.
Garin Albinen na kasar Switzerland inda ake biyan mutane kudi in sum koma da zama-boredpanda
Yanayin garin yana da matukar ban sha’awa, ga korayen ganyaye, ga tsaunika, da alama za’a samu yanayi me kyau.
Garin Albinen na kasar Switzerland inda ake biyan mutane kudi in sum koma da zama-boredpanda
Saidai babu mutane sosai da kuma abubuwan more rayuwa irin na birane, mutum zaisha zaman kadaici.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Kalli Bidiyo: Shi Ma Fa Aminu Ya Ci Kudin Talakawa Domin An Dana Shi A Jirgin Gwamnati

boredpanda

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *