Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana cewa basu da inda zasu cigaba da ajiye tubabbabun ‘yan Boko Haram da iyalansu a Maiduguri.
Domin yace gabadaya sansanin da suka gina masu guda uku duk sun cika makil babu wurin saka wasu mutane.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar litinin yayin daya ke kaddamar da kwamitin da zata dawo da ‘yan jihar da sukayi gudun hijira zuwa Chadi, Nijar da kuma Kamaru.
Sannan ya kara da cewa ya tattauna da shugaban rundunar hadakar jami’an tsaro ta hadin kai sun tattauna don gina manyan sansanin da za’a cigaba da ajiye su a ciki.
Kuma yace dole gwamnatin na bukatar tallafi daga wurin kungoyoyi masu zaman kansu da kuma kungiyoyin gwamnati, sannan a karshe yace kasar jamus ta bayar da tallafin yuro miliyan 15.