fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Ganawar gwamnati da ‘yan Bindigar da suka sace fasinjoji jirgin kasa ta samu koma baya yayin da gwamnati taki yadda ta saki shugabansu

Alamu na nuna cewa an samu koma baya wajan tattaunawar da ake tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan Bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasar dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja.

 

Hakan ya farune saboda kin amincewar gwamnatin kan sakin shugaban ‘yan Bindigar.

 

Akalla mutane 100 ne ke hannun ‘yan Bindigar wanda suka sace daga jirgin kasar.

 

Hukumar jirgin kasa ta Najeriya ta bayyana cewa akawai mutane 163 da kuma ma’aikatanta 7 da ba’a san inda suke ba.

 

Karanta wannan  Rundumar sojin sama sun hallaka shugaban 'yan ta'addan Boko Haram da tawagarsa a jihar Maiduguri

‘Yan Bindigar sun nemi a saki Shuwagabanninsu da kuma masu daukar nauyinsu 16 idan ana son su saki mtanen da suke rike dasu.

 

Saidai gwamnati ta ki amincewa da wannan bukata tasu.

 

Wata majiya ta bayyanawa Punch cewa, amma gwamnati na duba yiyuwar kubutar da mutanen ta wata hanya daban, misali, biyan kudin fansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.