Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya bayyana cewa manema labarai basu masa adalci ba kan kalaman da gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi akansa na cewa zai fadi zabe.
Gwamna Ganduje a ziyarar da Gwamna Wike ya kai masa a Kano yace gwamna Wike ba zai ci zaben shugaban kasa ba amma yayi kokari da ya fito takara.
Saidai Wike a hirarsa da BBC Pidgin ya bayyana cewa raha suke tsakaninsa da Ganduje.
Yace shine ya fara gayawa Gwamna Ganduje cewa, jam’iyyar APC ta gaza kuma shi ya zo ne ya kwace mulki daga hannunta.
Hakanan kuma ya bayyana cewa, to shine da Gwamna Ganduje ya karbi abin maganar ya rama.