fbpx
Friday, July 1
Shadow

Ganduje ya daƙile ficewar Barau daga APC ya kuma bar masa takarar Sanata

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya janye takarar sa ta Sanata bayan sulhu da su ka yi da Barau Jibrin, Sanatan Kano ta Kudu.

Rahotanni sun baiyana cewa Barau Jibrin ya gana da shugabannin jam’iyar NNPP a kwanan nan domin sauya sheƙa zuwa jam’iyar daga APC.

Tun da fari, Jibrin ya bi tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau su ka kafa wani tsagin na APC mai suna G-7.

A kwanan nan ne Ganduje ya sayi fom ɗin takarar Sanatan Kano ta Arewa domin ya maye gurbin Barau, wanda shi ka ya sayi fom ɗin duk da cewa bai bar APC ba.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Gwamna Wike zai ganada Bola Ahmad Tinubu a kasar Faransa

Sai dai kuma majiyar mu ta baiyana cewa tuni Ganduje da Barau su ka sasanta, inda tuni ma gwamnan ya janye wa Sanatan takarar.

Sakataren jam’iyar APC a Kano, Zakari Sarina, ya tabbatar da batun ga manema labarai a yau Litinin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.