Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mika mulkin jihar ga mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna bayan ya tafi kasar larabawa ta UAE.
Kwamishin yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan inda yace Gamduje zai halarci wani babban taro ne a kasar larabawan.
Kuma yana kira ga manyan jihar da shuwagabanni dasu baiwa mataimakin nasa hadin kai.