fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Ganin Wata: Waye akan daidai>>Sadiq Sani Sadiq ya tambaya

Tauraro fina-finan Hausa,  Sadiq Sani Sadiq ya bayyana rashin rashin dadinsa kan yanda aka samu rabuwar kawuna kan ganin Watan Shawwal a bana.

 

Sarkin Musulmi dai ya bayyana cewa ba’a ga wata ba inda ya bukaci al’umma su cika Azumi 30.

 

Yayin da shi kuma Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa sun ga wata kuma suka yi Sallah a yau.

 

Tun a jiya dama an Samu ‘yan Shi’a sun yi Sallarsu inda sukace suma sun ga watane shiyasa suka yi.

 

“Sadiq Sani Sadiq da yake bayyana rashin jin dadinsa ta shafinshi na Instagram ya Rubuta cewa, ina Marukar Bakin ciki, ranar da ya kamata mu kasance cikin farin ciki amma wallahi ina takaici irin wannan rabuwar kai da muke samu daga malaman addini wanda ya kamata akwai hadin kai koda kuwa akwai banbancin akida tunda dukkaninmu Allah daya muke bautawa…Innalillahi wa inna ilaihi raji’un wannan shekara dai ta zo da jarrabawa Mummuna ga al’ummar musulmin Duniya”

An dai samu Rahoto daga baya cewa kwamitin ganin wata suna neman wanda suka ce sun ga watan Shawwal.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *