Ganyan Rama ganye ne da Mazauna Arewacin Najeriya ke amfani dashi ta hanyar sarrafashi wajan yin abubuwa daban-daban kama da kwadantashi yin dambu dashi yin miya da sauransu.

Baya ga haka ganyan rama na tattare da Al’fanu da dama ga lafiyar jikin Dan Adama.
Ganyan Rama yana dauke da sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin kashi, hakanan Yana taimaka wa wajen wanke ciki.
Ganyen rama na magani da kare mutum daga cutar sida ko kuma daji kowanne iri ne.
Ganyen rama yana dauke da sinadarin ‘Vitamin A,B,C,D da B-12 dake kara karfin ido, saurin nika abinci a cika, sa jikin mutum warkewa musamman idan an sami rauni sannan ya na kara jini a jiki.
Rama na taimakawa wajen hana tsufa da wuri, Yana kuma rage kiba a jiki.
Rama tana kawar da bugawar zuciya na farad daya, haka zalika tana taimakwa wajan kawar da ciwon siga.