Gwamnan dai ya shafe kusan wata guda yana jinyar cutar korona bayan ya kamu a ƙarshen watan Maris, kafin sanar da warkewarsa daga bisani.
Ya ce gwamnati ta umarci mutane su riƙa sanya takunkumi a duk lokacin da suka fito daga gida, “amma mutane sun ƙi ji”.
Yanzu in ka fita kana garin Kaduna, mun ce duk wanda ya fito daga gidansa, ya sa takunkumi, ya sa facemask, mutane ba sa sawa, cewar Elrufa’i. “In ka tsayar da mutum ka ce ya bai sa ba. Sai ya fito da ita daga aljihu. (Ya ce) yana da ita”.
Gwamnan ya ce takunkumin wata kariya ce daga kamuwa daga ƙwayar cutar korona, kuma yana hana yaɗa cutar ga wasu mutane, idan mutum na ɗauke da ita.
An kuma tambayi Nasir Elrufa’i kan sane da halin da jama’arsa ke ciki musamman ma ‘yan kasuwar jihar da ake ta raɗe-raɗin cewa sun fara bara, sai ya ce: “Sun fara bara?” Amma ai gwamma yin bara da mutuwa, in ji shi.
“Gara kai bara kana da rai, da ka mutu… Hakkin da Allah ya ɗora mana a jihar nan, (shi ne) mu kare lafiya da rayukan ɗan’adam. Kasuwanci za a iya tallafa musu,” cewar Malam.
Idan komai ya koma daidai, za mu samu yadda za mu tallafa musu domin a koma harkokin kasuwanci kamar yadda aka saba a baya, gwamnan ya alƙawarta.