fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Gargadi!!! Bidiyon na da tada hankali: Kalli yanda wasu Samari suka zane ‘yan mata da Dorina sannan suka musu Aski a jihar Bauchi, ‘yansanda sun sha Alwashin daukar mataki

Wani bidiyo da ya nuna yanda wasu samari a jihar Bauchi suka zane ‘yan mata da dorina sannan suka wa wasu daga ciki Aski da reza ya bayyana a shafukan sada zumunta.

 

Bidiyon ne matukar tada hankali ga duk me Imani ya dauki hankula inda aka ji matasan na zargin ‘yan matan da cewa sun aikata musu ba daidai ba.

 

An rika dauko ‘yan matan daya bayan daya ana musu bulala.

 

Rahoton BBC ya bayyana cewa, Hukumar ‘yansandan jihar ta sha Alwashin daukar mataki akai da zai kai ga kama matasan.

 

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=183636723544879&id=100056956577045

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta ta fara bincike kan wani bidiyo da ya yaɗu a intanet kamar wutar daji, da ke nuna yadda wasu matasa suka dinga zane wasu ƴan mata da dorina.

Karanta wannan  Mutane 18 sun mutu sakamakon hadarin mota akan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

A sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce an ja hankalinta ne kan wannan bidiyo, inda ta jajantawa waɗanda lamarin ya faru da su, tare da shan alwashin gano waɗanda suka aikata wannan abu da gurfanar da su gaban shari’a.

Sanarwar me ɗauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Mohammad Wakil ta ce tuni rundunar ƴan sandan ta gayyaci ƴan matan da abin ya shafa da su bayar da bayanan da za su kai ga kama tare da gurfanar da samarin a gaban shari’a.

Bidiyon yana nuna yadda wasu zaratan matasa ɗauke da dorina da adduna a hannayensu suka rutsa wasu ƴan mata wani kango.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.