fbpx
Friday, August 12
Shadow

Garkuwa da shugaba Buhari da El Rufa’i tamkar garkuwa da matsalolin Najeriya ne, Omokri yace sauki ‘yan bindiga ke nemawa Najeriya

Mai sharhi akan labaran siyasa, Reno Omokri yace sauki ‘yan bindia ke nemawa al’ummar Najeriya sai yasa suka ce zasu yi garkuwa da shugaba Buhari da gwamna El Rufa’i.

Reno Omokri ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook inda yace idan har sukayi garkuwa da Buhari tamkar sunyi garkuwa da matsalolin Najeriya ne.

Domin shugaban kasar ya samu Dala akan Naira 190 amma yanzu Dala ta hauhawa har zuwa Naira 650, saboda haka garkuwa dashi tare da El Rufa’i sauki ga al’ummar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.