fbpx
Monday, December 5
Shadow

Gasar cin kofin Duniya 2018: Messi yayi kaca-kaca da Najeriya

Tauraron dan wasan kwallon kafan kasar Argentina, Lionel Messi ya bayyana matsalar ‘yan wasan Najeriya a lokacin wata hira da akayi dashi inda aka tambayeshi me zaice dangane da kasashen da aka hada kasarshi rukuni daya dasu a gasar cin kofin Duniya da za’a buga a kasar Rasha shekarar 2018 idan Allah ya kaimu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Messi ya bayyana wa hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA, ta Yanar gizo cewa, Su matsalar ‘yan Najeriya shine, yau zasu yi wasa me kyau, suci kwallaye hudu, amma wataran kuma sai su barmaka fili kayi yanda kake so.
Amma akan sauran kasashen dake rukunin, watau Croatia da Iceland Messi yace, Iceland za’a gansu kamar suna da saukin wasa amma sun da wuyar wasa tare kuma sun da tsari me kyau. Akan Croatia kuwa mesii yace, Suma suna da ‘yan wasa masu kyau kuma sun bayar da dama a taba kwallo da kyau.   


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  An buɗe tsohon babban birnin Saudiyya domin masu yawon buɗe ido

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *