fbpx
Wednesday, October 21
Shadow

Getafe 1-0 Barcelona: Jamie Mata ya taimakawa Getafe da penariti yayin da Barcelona ta yi rashin nasarar farko a bana

Barcelona ta fadi wasa karo na farko a wannan kakar bayan Ronald Koeman ya jagoranci kungiyar tayi nasarar cin wasannin ta guda uku da suka gabata a jere, kuma Barcelona tayi kokari kafin aje hutun rabin lokaci yayin da har ta kai hari sau daya amma ta kasa cigaba da kokarin bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

A karshe an tashi wasan ne Getafe tana cin 1-0 bayan Jamie Mata yayi nasarar cin penariti a minti na 56. Karo na biyu kenen da Barcelona da Real Madrid gabadaya suka fadi wasannin su ba tare da zira kwallo ko guda ba a rana guda cikin shekaru 30 da suka gabata bayan sun yi hakan a shekara ta 2000 watan mayu.
Rabon Barcelona da Real Madrid su fadi wasan kafin su buga El Classico tun shekara ta 2003 ne yayin da Madrid ta sha kahi 4-2 a hannun San Sebastian itama Barcelona ta sha kashi 4-2 a hannun Deportivo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *